Wani Tsohon Janar, General Ali Keffi ya bayyana cewa, masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya ne sun ka haddasa hadarin da ya kashe tsohon shugaban sojoji, General Ibrahim Attahiru.
General Danjuma Ali Keffi mai murabus wanda shi ne tsohon shugaban runduna ta ɗaya ta sojoji da ke kaduna ya bayyana haka ne
Ya ce an ƙi yin binciken haɗarin jirgin ne saboda wasu masu ɗaukar nauyin harkar ta’addanci ne sun ka haddasa hatsari da ya kashe shi.
Ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya gudanar da bincike a kan haɗarin jirgin kuma a kama tare da hukunta duk wanda an ka samu da laifi.