Uwar Hausawa ƴan gwagwarmaya Kaltum Alumbe Jitami ta ƙara rubuta wata sabuwar waka ta kishin Hausa da Hausawa a matsayin kabila, sannan sai kishin ƙasar mu Nijeriya.
A baya ta rubuta waƙa ta farko, ta biyu da ukku waɗanda sun yi tashe, yanzu kuma ta ƙara gwagwaje muku wata dan ku shaƙata ku faɗaka.
Wakar mai taken komi nisan jifa sai ta yo kasa ta ƙayatar sosai, kuma ta bada ma’ana dangance da zamantakewa, hadin kai, tarihi, al’adu, da rayuwar Hausawa da yan Nijeriya baki ɗaya.